Kannywood

Maimaita kuskure shima kuskure ne – Darasin da Zango zai iya koya daga auren da ya gabata

Maimaita kuskure shima kuskure ne, kamar yadda wani yayi rubuta a shafinsa na sada zumunta game da Adam A. Zango da auren da ya yi.

Tabbas wannan magana gaskiya ce, domin idan aka yi la’akari da tasirin maganganun jama’a akan rayuwar auren Adam A. Zango, lokaci ya yi da ya kamata ya rage wallafa matarsa a kafafen sada zumunta, musamman hotuna ko bidiyo na rungume-rungume.

Yawancin matan da ya aura a baya sun shiga irin wannan rayuwa na hotuna da bidiyo a lokacin birthday, sallah ko wasu lokuta na musamman.

Ba wai cewa hakan shi ne babban dalilin rushewar aurensa ba, amma da zai dan rage ko kuma ya daina wallafa irin waɗannan abubuwa, watakila ya sami rangwamen magana da surutan jama’a.

Domin abin da ake cewa kambun ido ko kambun baka, shi ake ɗauka a matsayin gaskiya.Muna fatan Allah Ya sa wannan aure ya zamo na karshe ga amarya, mutuwa kaɗai ce za ta raba ta da mijinta. Amma ga shi kuwa, ba za mu yi fatan wannan shi ne auren ƙarshe ba, sai dai mu yi masa fatan kari da karin albarka a duk wani aure da zai yi nan gaba, in sha Allah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button