Amina Uba ta zargi tsohon mijinta Adam A. Zango da zama cikas a shigarta cikin Kannywood.

Fitacciyar jaruma Amina Uba, wacce aka fi sani da Jamila Labarina, ta bayyana yadda suka yi da tsohon mijinta Adam A. Zango a lokacin da take neman damar shiga masana’antar Kannywood.A cikin shirin Gabon Talk Show, Amina ta ce ta bawa tsohon mijinta girma da mutuncinsa saboda ɗan da ke tsakaninsu, har ma ta nemi shawarar sa kafin ta fara fim.
“Ai fim sana’a ce, idan kika ɗauke shi sana’a. Marainiya ce ke ba ta uba ba ta uwa. Duk abinda za ki yi, ki ringa duban kanki, marainiya ce ke. Saboda iyayenki suna ƙasa.
Ki tuna ke uwa ce, ki kare mutuncin ɗanki. Kannenki suna gidan miji, ki kare musu mutunci.
”Ta ce waɗannan su ne shawarwarin da Adam A. Zango ya bata kafin ta shiga harkar fim.Sai dai daga baya, bayan da ta fara mu’amala da masu shirya fina-finai, labari ya chanja.
Ta bayyana cewa an dinga ja da baya da ita, abin da ya sa ta gane asalin matsalar, wanda a cewarta shi ne tsohon mijinta Adam A. Zango.Duk da haka, Amina ta jaddada cewa Allah ya taimake ta, kuma yanzu tana taka rawar gani a masana’antar Kannywood, duk da ƙalubalen da ta fuskanta a farko.









