Kannywood
Jaruman Kannywood Biyu Da Ake Zargin Ƴan Shi a Ne

Fitattun jaruman Kannywood guda biyu — Ali Hussain wanda aka fi sani da Sahabi a cikin shirin Kwana Casa’in na tashar Arewa24, da Aisha Najamu — sun janyo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta bayan wasu hotuna da bidiyo suka bayyana suna nuna alamar bin akidar Shi’a.
A cewar rahotanni, da farko mutane da dama ba su san cewa Ali Hussain na daga bangaren Shi’a ba, sai bayan da aka ga hotunansa a cikin baƙaƙen kaya tare da wasu ‘yan Hisba. Wannan ya jawo martani daga masoyansa da suka nuna rashin jin daɗi.
Haka zalika, Aisha Najamu ta bayyana kanta a fili ta hanyar wallafa abubuwan da suka shafi Shi’a a shafinta na sada zumunta, lamarin da ya ba mutane mamaki tun daga lokacin da ta fara yin hakan.