Wani mutum ya ƙone bayan fashewar fawa bank ɗinshi

Wani mutum ya mutu sakamakon ƙonewar da ya samu a filin jirgin saman Melbourne na ƙasar Australia bayan da na’urarsa ta fawa bank – da ake caji da ita – ta fashe.
Mutumin mai shekara 50 na cikin babban zauren da fasinjoji ke jiran jirgi, a lokacin da na’urar cajin tasa ta kama da yahaƙi, lamarin da ya tilasta wa mutanen da ke cikin zauren kusan 150 gaggawar ficewa, kafin fashewartaMa’aikatan filin jirgin sun kai wa mutumin taimakon gaggawa kafin a garzaya da shi asibiti, inda ya mutu a can.
Kamfanin jirgin sama na Qantas – da mutumin zai shiga – na nazarin dokokinsa kan barin fasinjoji su riƙe na’urar fawa bank, inda ake sa ran zai fitar da sabbin dokoki a nan gaba.
Kamfanonin jiragen sama da dama na shawartar fasinjoji kan riƙe na’urar fawa bank, a lokacin da za su shiga jirgi.
A watan Yuli ma na’urar fawa bank ta haddasa tashin hayaƙi a cikin wani jirgin kamfanin Virgin Australia da ya tashi daga birnin Sydney zuwa Hobart.Haka ma watan Janairun wannan shekara na’urar ta lalata wani jirgin fasinja a Koriya ta Kudu.









