Uncategorized

Shirin Fim Ɗin Hausa Mai Dogon Zango Na Farko da Sama Mutum Miliyan Daya Suka Kalla Cikin Kwana Hudu.

Ƙudiri sabon shirin fim ne mai nisan zango wanda ya sha bambam da waɗanda ake kallo.

Shiri ne da aka zuba basira da lissafi wanda ke ƙunshe da zunzurutun fikira kamar irin finafinan da suka yi suna a duniya na ƙasashen ƙetare.

Ƙwaƙwalwa ta taka muhimmiyar rawa a shirin, yayin da masu laifi suka aikata kisan kai suka toshe duk wata hujja da za a gano su, a lokacin su kuma ƙwararrun jami’an tsaro suka zurfafa bincike cikin ƙwarewa. SƘudiri, idan ka fara kallonsa ba za ka daina ba, idan ka kammala kallon na wannan makon za ka shafe mako guda cike da zumuɗi da ɗokin Alhamis ta zagayo domin ci gaba da kallon inda aka tsaya.

Sababbin fuska ne a cikin shirin amma saboda ƙayatuwarsa ya kafa tarihin da babu sabon shirin da ya taɓa kafawa. Inda ya sami mabiya sama da miliyan ɗaya cikin kwana huɗu kacal.

Tabbas Ƙudiri sai ya danne duk wani shiri mai dogon zango da yake tashe a duniyar finafinan Hausa. Domin shiri ne da ya zo da sabon salon da ba a taɓa ganin irinsa ba, ya zo da darusan rayuwa mabanbanta.

Shiri ne da hatta jami’an tsaro sai sun ƙaru da ilmin cikinsa na bincike, basira, fikira da lissafi balle kuma sauran jama’ar gari.

Da a ce ana shiri irin na Ƙudiri da Kannywood ta yi zarra a duniyar finafinai ta duniya, domin mafi yawancin shirye-shiryen Kannywood ana yinsu ne kan soyayya, shaye-shaye ko daba amma shi Ƙudiri na daban ne ya zo da wani salo da yake wahalar bayyanawa a baki dole sai mutum ya gani da kansa zai fahimta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button