Tsohuwar Matar Adam A Zango ta yi karin bayani kan furucinta na aure da “mutumin da bai dace ba

Ameena Rani wacce aka fi sani da Jamila Labarina ta yi karin bayani kan furucinta na cewa ta auri mutumin da bai dace ba a lokacin da ya dace.
Ta yi wannan furuci ne a dandalin Hadiza Gabon, wanda ya jawo ce-ce-ku-ce har masoyanta suka rika jan hankalinta kan batun.
Wannan ne ya sa ta ga dacewar fito da karin haske.A cewarta, kalaminta na cewa ta auri mutumin da bai dace ba — “She got married to a wrong person at the right time” — ba nufin cin mutunci ko zagin wani bane.
Tana nufin da ace Adam A. Zango shi ne wanda ya dace, da yanzu suna tare, haka zalika da ita ce ta dace da shi.Game da kalmar “a lokacin da ya dace” kuwa, ta bayyana cewa tana nufin ta yi aure ne tun kafin ta kai shekara 20, kuma hakan ya ba ta damar samun ƙaruwa da ci gaba a rayuwarta.