Duk wani ɗan TikTok dole ne yaje a tantance bidiyonshi kafin ya ɗaura a TikTok – Abba El Mustapha

Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano ta sanar da fara yin rajista ga masu amfani da kafar TikTok a jihar, domin tantance su da tabbatar da bin dokoki da ka’idojin jihar.
Kakakin hukumar, Comrade Abdullahi Sani Sulaiman, ya bayyana hakan a wata tattaunawa da gidan talabijin na ARTV, inda ya ce wannan mataki na daga cikin manyan nasarorin da shugabancin hukumar ƙarƙashin Abba Almustapha ya cimma kwanan nan.
A cewarsa, rajistar za ta taimaka wajen kare al’ummar Kano daga masu amfani da kafafen sada zumunta wajen yada abubuwanda ke saɓa tarbiyya da al’ada.
Ya ce hukumar na son samar da tsari da zai tabbatar da cewa masu amfani da TikTok suna bin doka yayin samar da abun cikin su.
Kakakin hukumar ya ƙara da cewa masu TikTok za su iya yin rajistar ne ta mutum ɗaya-ɗaya ko kuma ta ƙungiyoyi, gwargwadon yadda suka ga dama.
