Kotu bata da hurumin yiwa mutane auren dole – Kungiyar Lauyoyi

A cikin makonnin baya-bayan nan, wata kotun Majistare da ke jihar Kano ta yanke hukunci da ake cewa ya tilasta auren Ashiru Idris Maiwushirya da wata mata mai suna Basira Ƴarguda.
Wannan hukunci ya janyo ce-ce-ku-ce a fadin ƙasar nan, musamman daga ɓangaren ƙwararrun lauyoyi da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam.Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya wato NBA – ta bayyana wannan mataki a matsayin tauye haƙƙin bil’adama, tare da cewa ya ci karo da dokokin kasa da kuma kundin tsarin mulki. Sun ce kowane mutum yana da ‘yancin zaɓar wanda zai aura, kuma kotu ba ta da hurumin tilasta aure tsakanin mutane ba tare da yardar su ba.
A cewar NBA, wannan hukunci zai iya rage amincewar da jama’a ke da ita ga shari’a da kuma kotuna, domin adalci ba wai kawai a yi shi ba ne, sai an yi shi a bayyane kuma bisa ka’ida.
Ƙungiyar ta kuma bukaci kotunan Najeriya da su rika bin ka’ida da kare mutuncin ɗan adam, musamman a shari’o’in da suka shafi aure da zamantakewar al’umma.









