Shugaban Kasar Nijar Ya Tallafa Wa Jarumin Kannywood Malam Na Tala’ala

Shugaban mulkin sojin Jamhuriyar Nijar, Janar Abdoulramane Tchiani, ya nuna jinkansa ga jarumin Kannywood, Malam Na Tala’ala, wanda ke kwance a gadon asibiti.
Malam Na Tala’ala ya bayyana hakan a wani bidiyo da ya fitar, inda ya tabbatar da cewa Shugaban ƙasar ya kira shi ta waya don jin halin da yake ciki.
A cewarsa, Janar Tchiani ya kuma tura masa tallafin kuɗi don rage masa radadin rashin lafiya, sai dai jarumin ya ce ba zai bayyana adadin kuɗin ba a halin yanzu.
Tallafin daga Shugaban mulkin sojin Nijar na zuwa ne a daidai lokacin da masana’antar Kannywood ke fuskantar ƙalubale, musamman ta fuskar tallafi da jin ƙai ga jarumanta da ke cikin matsaloli na lafiya ko tattalin arzikiAllah ya kara mishi lafiya da duk wanda bashi da ita.
Ya kuma ci gaba da rufa mana asiri amin.









