Abinda Yake Faruwa

Aisha Yesufu Ta Ce Musulmai Su Mayar da Kano Hannun Maguzawa da Kiristoci, Ta Ce Asalin Kano Ba Ta Musulunci Bace.

Wani sabon jawabi da aka danganta da Aisha Yesufu ya janyo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta.

A cikin jawabin da aka yada daga shafin northern_scope, an bayyana cewa Aisha ta yi kira ga Musulman Jihar Kano da su bar garin su ba wa Maguzawa da Kiristoci damar mallakar garin, tana mai cewa asalin jihar Kano ba ta musulmai bace.

Aisha Yesufu ta ce Maguzawa da Kiristoci su ne asalin mazauna jihar Kano kafin Musulmai su mamaye garin. Ta kara da cewa musulmai sun karbe garin ne ta hanyar auren mata da yawan haihuwa, wanda hakan ya ba su damar cika Kano da Musulunci.

Jawabin ya janyo martani daga jama’a daban-daban, musamman saboda kalaman suna da zafi kuma suna iya tayar da hankali dangane da addini da asalin mutanen yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button