Abinda Yake Faruwa

Watan mu 13 da aure amma sau 10 kacal ya taɓa saduwa dani

Assalamu alaikum Malam, barka da dare. Sunana Rukayyat Haruna. Munyi aure da mijina fiye da shekara guda (wato wata 13), amma abun damuwa ne saboda sau 10 kacal ya taba saduwa da ni tun bayan aurensu.

Shi matafiyi ne, yana zaune a Legas yana neman kudi. Duk lokacin da ya tafi, zai iya shafe watanni shida bai dawo gida ba, sai dai kawai ya turo min kudi.

Tun da muka yi aure sau daya ya dawo, kuma duk satin da ya yi a nan gida guda daya ne kafin ya koma. Har yanzu bai dawo ba.

Ni kuma mabukaciya ce, amma ina kamuwa da hakuri don mutuncinsa.

Na kai kara gidanmu na nemi ayi min adalci, nace ina son a raba auren saboda bana samun hakkina na saduwar aure. Ina so in auri wanda zai cika wannan hakki domin hakan yana da muhimmanci a rayuwata.

Amma iyayena sun hana, suna bukatar in ci gaba da zaman auren. Wannan ya sanya ni cikin wani hali mara dadi. Don Allah ku taimake ni da shawara.

Idan wani daga cikin daliban wannan shafi ya ga wannan sakon, don Allah ku turo min da shawarar da bata zalunci ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button