Abinda Yake Faruwa

Ahmed Xm da Tsohuwar Matarsa Safiya Sun Halarci Bikin Haihuwar Ƴarsu Cikin Kwanciyar Hankali

Yau an hangi Ahmed Xm tare da tsohuwar matarsa, Safiya, a wajen bikin zagayowar ranar haihuwar ƴarsu.

Duk da cewa sun rabu a matsayinsu na ma’aurata, sun bayyana tare da farin ciki da kulawa domin murnar wannan rana ta musamman ga ‘yarsu.

Taron ya gudana cikin natsuwa da farin ciki, inda duka biyun suka kasance kusa da ƴarsu, suna nuna soyayya da kulawa kamar yadda iyaye nagari ke yi.

Wannan hali nasu ya janyo yabo daga dangi da abokai da suka halarta, inda da dama suka bayyana jin daɗin ganin yadda suka ci gaba da kasancewa uwa da uba masu fahimta duk da banbance-bambancen da suka raba su.

Wannan ya zama abin koyi ga wasu iyaye da suka rabu cewa komai ya faru a tsakaninsu, kula da yaransu da zaman lafiya na iya ci gaba da kasancewa babban ginshiƙi a rayuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button