Maganar Da Jarumi Ramadan Both Yayi Tsantsar Gaskiya Ce Baiwa Butulci Ba

Tun bayan wata hira da kayi da jarumi Ramadan both daya ce Jarumi Ali Nuhu ba Uban gidansa bane Kasuwanci ne ya hadasu Ake gani lafinsa tare da kiransa butulu Wanda ya butulcewa uban gidansa magana ta gaskiya ba’ayiwa Jarumi Ramadan adalci ba Kuma abin daya fada gaskiya ne Darakta Imrana I Ashir shine Wanda yasoma yi masa film sannan Kuma shine Uban gidansa daya haskashi duniya ta sanshi daganan shikuma Jarumi Ali Nuhu ya ganshi ya daukoshi domin yayi masa aiki film yakuma biya shi hakkinsa.
Abi danake so mutane su gane anan shine Ramadan both Jarumi ne kawai shikuma Ali Nuhu Darakta ne sannan Kuma Jarumi Wanda yake da Kamfani da zai iya dauko kowanne jarumi Suyi masa aiki film sannan ya biyasu hakkisu kowa ya kama gabansa.
Kunga kenan Kasuwanci ne ya hadasu ta dalilin Uban gidansa Imran I Ashir domin shima Ali Nuhu anan ya ganshi har yaga dacewar yin aiki dashi domin da Bai hango riba ajikin Ramadan both babu yadda za’ayi ya sanya kudinsa wajan shirya masa film kokuwa Sanya shi acikin film sa ana wajan idan nace kowa ya taimaki kowa banyi karya ba tamkar Mai siyane dakuma Mai siyarwa.
Kamar yadda Jarumi Ali Nuhu ya dauki Ramadan both yayi masa aiki film ya sallameshi haka Shima Jarumi Ramadan both yake dauka Ali Nuhu yayi masa aikin film yakuma biyashi kudin aikinsa wannan shine Kasuwanci na gaskiya baiwa batun maganar Uban gida ba.
Ga Dan wani misali wanda zaku yadda cewa tsakanin Ali Nuhu dakuma Ramadan both Kasuwanci ne kawai ya hadasu shine Yaro ne aka kaishi gurin koyan dinki har ya iya wannan dinki agurin Wanda ya koya masa wata rana sai wani Abokin ubangidan nasa yazo yaga yaga yadda yake aikinsa sai ya kirashi zuwa nasa shagon domin yayi masa wasu ayyuka ya biyashi daganan Alaqar su ta kullu sosai yaci gaba da yimasa ayyuka Yana biyansa shin idan akan tambayi wannan yaro wanene Ubangida Wanda ya koyamaka aiki ne har ka Iya mutane suka gani kokuwa Wanda yaga Kwarewar ka ya daukeka aiki Yana biyanka idan ka gama idan aka tambayeka waye Uban gidanka cikin su was zakace?









