Abinda Yake Faruwa
Na je gidan yar uwar saurayina bisa gayyatar sa, amma sai suka haɗa baki domin su cutar da ni.

Da farko aka kawo min lemo mai sanyi, amma zuciyata bata amince ba. Na shiga bayi sai na ji saurayina yana cewa yar uwarsa ta tabbata na sha.
Da na fito, yar uwar tasa ta fita, shi kuma ya matsa min akan sai na sha.Na gane shirinsu, sai na ce masa: “Ka ji tsoron Allah! Kaima kana da ‘ya mace, duk abin da ka kai wa wani, sai an yi maka.
”Ya so ya yi mini ta karfi amma Allah ya kare ni. Sai yar uwarsa ta dawo, daga nan na fice daga gidan cikin gaggawa.Ku sani, ba kowanne gayyata ake amsawa ba.
Ku yi addu’a, ku kuma ji tsoron Allah a dukkan lamurra.









