Kannywood
Da za a dinga shirya fina-finan Kannywood yadda manyan masana’antu kamar Hollywood da Bollywood ke shirya nasu, da yanzu mun wuce su

Saboda Kannywood tana da abin da ya bambanta ta al’adu, tarbiyya da kuma ɗauke da darasin addini.
Abubuwan da idan aka yi musu kwalliya da tsari irin na zamani, da sun kai mu gaban duniya.
Idan aka kara kulawa da Ingancin labari da kayan aiki, Horas da ‘yan wasa da masu shirya fim, Kare haƙƙin mallaka, Da kuma tallata fina-finai a manyan dandamali na duniya, babu shakka za mu ga Kannywood na tunkarar gaba, har ta fi sauran masana’antu armashi da tasiri.









