Kannywood

Facebook Page Dina Shine Shagona – Baba Sadiq

Wani lokaci, mutane basu fahimci girman da harkokin social media suka samu ba, musamman a fannin kasuwanci.

A yau, Facebook page na iya zama kamar wata kasuwa da kake buɗewa domin ka sayar da kayanka, kamar yadda kowane ɗan kasuwa yake yi.​Na riƙe Facebook page ɗina, kuma shine ya isheni duniya. Ina yi muku addu’a, musamman ga waɗanda suke cewa “zuciyata ta mutu” saboda ba su fahimci ba.

Ku sani, kamar yadda kake buɗe shago a kasuwa domin samun riba, haka ma page ɗina yake. Ba aikin banza nake yi ba. Harkokin social media su ne sana’a ta, kuma ban da haka, nakan taimaka wa wasu yan kasuwa su tallata kayansu, wanda hakan ke ƙara kawo mini riba.

​Muhimmancin Abin da Ka Ke Sakawa (Content)​Kuna iya yarda ko ba ku yarda ba, amma duk wanda yake sakawa da abubuwan da zasu jawo hankalin mutane (engaging content) a Facebook, to lallai ba karamin mutum bane, musamman idan ya san abinda yake yi.​

Na san cewa dole ne mu bai wa al’umma abinda suke so. Tunda wannan ne abinda ku(audience) kuke so, to fa haka zamu dinga kawo muku. Ga duk wanda yake ta zagina amma yana ta kasancewa tare da ni, ina sanar da shi cewa ina sane da yanayinka ko kin cika.

​Girmama Zaɓin Kowa​Na san cewa ba za ka iya gamsar da kowa ba, domin mutum sai Allah. Amma ina so ku sani, yanzu aka fara, babu gudu babu ja baya. Sai inda Allah ya tsara. Duk wanda abun da nake sakawa bai masa ba, don Allah, ya daina bin shafi na, ya yi “blocking” domin ya samu kwanciyar hankali, kada ciwon zuciya ya same shi.​

Ba za mu tara mutane mu zauna kawai ba, sai dai mu cigaba da ba su shawara yadda suma zasu dogara da kansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button