Abinda Yake Faruwa

Shahararren Makarancin Qur’ani A Social Media Ya Mallaki Sabuwar Mota

Fitaccen matashin ɗan Najeriya da ya yi fice wajen karanta Al-Qur’ani mai girma a shafukan sada zumunta kamar TikTok da Instagram, Young Alhajee, ya bayyana sabuwar motarsa a matsayin wata ni’ima daga Allah da kuma ci gaba a rayuwarsa.

Matashin, wanda ya shahara da kalar sautin karatunsa mai daɗi da ke burge masu sauraro tare da shakuwa da Qur’ani, ya wallafa hotunan motar a shafinsa na sada zumunta. A cikin rubutunsa, ya yi tsokaci kan yadda yake godewa Allah da kuma masoyansa da ke mara masa baya a kowane lokaci.

A wasu hotunan da ya bayyana, an hango shi cikin annashuwa yana mika godiya ga Ubangiji bisa wannan baiwa, tare da jaddada cewa wannan ya zama wata hujja ga matasa su ci gaba da rungumar addini da karatun Al-Qur’ani cikin tsoron Allah.

Masu bibiyar shafinsa da masoya da dama sun yi ta taya shi murna da addu’o’in alheri, suna bayyana farin cikinsu kan wannan ci gaba da ya samu, tare da fatan Allah ya kara masa albarka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button