Yaro Dan Shekara Goma 17 Yayi Min Ciki Ku Bani Shawara

Ina cikin damuwa mai girma saboda wani yaro dan shekara goma sha bakwai ya yi min ciki. Ni mace ce ‘yar shekara talatin da shida, mijina ya rasu, kuma na ci gaba da zama a gidansa tare da ‘ya’yana.
Wannan yaron dan makocina ne, shi ke yawan zuwa min gida yana taimaka min da aiki irin su gyara wuta.
Ni da kaina na fara neman shi saboda na dauka bai kai matsayin da zai iya yi wa mace ciki ba. Na kwana ina amincewa da shi har tsawon shekara guda ba tare da fargabar samun ciki ba, sai yanzu da na lura ban yi batan wata ba tsawon kusan wata biyar.
Bayan na je asibiti, likita ya tabbatar min da cewa ina da ciki mai kusan wata hudu da ‘yan kwanaki. Na sha kokarin ganin cikin ya zube amma hakan ya ci tura. Yanzu dai na yanke shawarar in tunkari iyayen yaron na sanar da su wannan hali da nake ciki. Idan kuma suka ki yarda su karɓi wannan lamari, ina ganin zan iya kai maganar kotu.
Don Allah ku ba ni shawara.









