Abinda Yake Faruwa

Matashi Ya Janye Aure Bayan Ya Iske Mahaifin Budurwarsa Yana Wanke-Wanke

An rawaito cewa wani saurayi a Najeriya ya fasa auren budurwarsa bayan ya kai ziyara gidansu, sai ya tarar da mahaifin budurwar cikin wanke-wanke, sannan mahaifiyar ta na ta hargowa tana hanzarta shi ya kammala aikin.

Wannan abu ya ba saurayin mamaki matuka, ya kuma fassara shi da cewa mahaifin bai da iko a gidan, matar ce ke juya shi. A ganinsa hakan na nuni da irin tarbiyyar da amaryar za ta tashi da ita, don haka ya yanke shawarar janye auren gaba daya.

To me za a ce game da wannan lamari? Shin yin aikin gida ga uba alamar rashin iko ne, ko kuwa nuna saukin kai da taimako ne? Kuma shin dacewa ne a raba aure saboda ganin uba na aikin gida, ko kuwa rashin hakuri ne daga bangaren saurayin?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button