Ƴan Kannywood Sunada Dabi’ar Bada Kudi A Wajen Biki Amma Basa Taimakawa Marasa Lafiyar Cikin Su

Yan Kannywood na da ɗabi’ar bada gudummawa sosai musamman idan aka je dinner ko wani biki. Amma abin mamaki shi ne, me ya sa a lokutan rashin lafiya ko lokacin da ake cikin tsananin buƙata ake ganin gudummawar ba ta da muhimmanci? Ko kuwa dole sai mutum ya rasu kafin a fahimci darajar taimako?A jiya ma, an shaida yadda aka rika bada gudummawar miliyan ɗaya, dubu dari biyar da sauransu wajen wani biki.
Amma idan aka waiwayi, akwai bayin Allah a Kannywood da suka mutu saboda rashin samun taimako na gaggawa, irin su Baba Karkuzu, Waragis, da Sani SK – Allah ya jikan su.Haka nan akwai waɗanda ke cikin matsanancin bukatar taimako a halin yanzu, kamar Malam Nata’ala da Alhaji Ayuba Dadin Kowa, amma suna fuskantar ƙalubale.
Wasu kuma kamar Idris Moda, sun shaida rashin lafiya, sai dai Allah ya kawo sauƙi.Haka nan akwai fitattun jarumai da suka cancanci a tallafa musu ba wai saboda rashin lafiya ba, amma saboda irin rawar da suka taka a masana’antar, misali Husaini Sule Koki.
Dukiya, kamar yadda ake faɗa, maganin mai ita ce, amma kamata ya yi a dinga kallon ɓangaren bukata da taimakon juna, ba wai kawai lokacin biki da shagulgula ba.Allah ya taimaki masu bukata, ya karawa mu rufin asiri a duniya da lahira.









