Abinda Yake Faruwa

Zarge-zargen Cin Hanci da Rashawa: Gwamnatin Abba Gida-Gida na da Nauyin Bayani – Abba Hikima

Mun yaki gwamnatin Ganduje ne bisa zarge-zargen cin hanci da rashawa. Saboda haka, idan yau gwamnatin Abba Gida-Gida ita ma aka zarge ta da makamancin hakan, to wajibi ne ta kare kanta da hujjoji masu karfi ko kuma ta bada dama a gudanar da bincike mai gaskiya, tare da hukunta wadanda ake zargi.

Ba hujja bace a ce “a lokacin Gandluje ma ga yadda ake yi” ko kuma “muna da lambobin yabo daga waje”.

Domin idan da Ganduje yayi dai-dai, da ba mu yi adawa da shi ba har karo biyu.

Abubuwan da ake magana a kansu sun haɗa da:

• Jawabin wanda ake zargi: A cikin jawabin kansa, akwai alamar amincewa da laifi, kuma kotu ta riga ta kwace wasu kudaden da ake zargi an sato.

• ICPC ta kwato kudade: Hukumar ta tabbatar da kwato sama da biliyan ɗaya, har ma aka mayar da kudin cikin asusun gwamnati.

• Kudin jama’a a asusun mutum ɗaya: Ana zargin wasu kuɗaɗen gwamnati sun shiga asusun mutum, daga bisani ya karkatar da su.

• Amfani da BDCs wajen karkatar da dala: Ana zargin an yi amfani da wasu dillalan canji a Abuja wajen karɓar dala fiye da abin da doka ta amince da shi, ba tare da bin ƙa’ida ba.

Wadannan abubuwa ba batun blanket denial bane. Su ne ya kamata gwamnati ta fito ta yi bayani a kansu, dalla-dalla.

Maganar cewa “’yan adawa ne suke son cin dunduniya” ma ba hujja bace. Aikin adawa kenan – su fito da zarge-zarge. Aikin gwamnati kuma shi ne ta kare kanta da gaskiya, ko kuma ta gyara inda aka samu kura-kurai.

Wannan kuma ba sabon abu bane, kowace gwamnati ana yi mata haka.Saboda haka, gwamnatin Abba Gida-Gida wadda ta zo da alƙawarin zero tolerance against corruption, tana da nauyin tabbatar da wannan alƙawari a aikace. Jama’a suna sa ran ganin tsabtaccen bayani da gaskiya, ba wai kawai maganganu na siyasa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button