Baana Yayi Zazzafan Martani ga Tsohuwar Jaruma Tumba Gwaska

Jarumi Baana ya yi wa tsohuwar jarumar Kannywood, Tumba Gwaska, martani mai zafi biyo bayan furucin da ta yi cewa jaruman yanzu ba su isa ta kira su ta yi musu magana ba.
Wannan magana ta fito ne a wata hira da aka yi da ita a gidan talabijin, inda mai hira ya jefa mata tambayoyi da wasu ke ganin da gangan aka yi don a tunzura ta.Sai dai kalamanta sun nuna kamar tana da ɗan kaikayi a ranta – watakila saboda irin tambayoyin da aka yi mata, ko kuma yadda ake ganin jaruman yanzu sun fi shahara, ita kuma an yi kamar an manta da ita.A martanin da Jarumi Baana ya yi, ya bayyana cewa:
“Ai abin da kayi dama an ce shi za a yi maka. Ita ma a zamanin ta ta zo a gabansu, kuma duk da cewa ba ta da wani dogon shuraa sosai a masana’antar, sai dai ta ɗan yi daidaiku. Don haka idan jaruman yanzu ba su ga girman ta ba, ba laifin kowa ba ne, tunda masana’antar haka take.
”Martanin Baana ya tayar da kura a tsakanin masoya fina-finai, inda wasu ke ganin gaskiya ne, yayin da wasu kuma ke ganin bai kamata ya maida mata martani da irin wannan salo ba.