Aikatau Ne Ya Kai Ni Kasar Saudiya

Yan uwa, wallahi ina cikin tashin hankali da dana sanin zuwa kasar Saudiyya domin aikin gida.Ni nake dafa abinci, ni nake wanke-wanke, ni nake share gida kullum aiki ne babu hutu.
Amma abin bakin cikin da ya fi komai, wani tsohon Balarabe ya soma zuwa baya na yana goga jikinsa da ni. Har ma wani lokaci sai ya kawo gabansa kusa da baki na. Wannan babban cin zarafi ne da ya sa ni kullum ina kuka.
Na kai korafi wurin wacce ta kawo ni wannan kasar, amma sai ta ce min “ki yi hakuri, yanzu aikin gida ya yi wuya a Saudiyya.” Amma ni ba zan iya ba, domin wulakanci da tozarci suke yi min kowace rana.
Abin da ya kara damuna, har yanzu ban gama biyan bashin kudin da aka ci don kawo ni nan kasar ba. Wannan yasa dole na cigaba da jurewa ko da a cikin tsananin bakin ciki.Wani lokaci har zuciyata tana raya min in kashe kaina kawai in huta, saboda abin da nake ciki ya wuce tunani.
Da na sani, da ban baro ƙasarmu ba. Da na zauna na yi aure cikin mutunci, na rufa wa kaina asiri.Yan uwa, ku tayani da addu’a Allah Ya kare mu mata daga irin wannan wulakanci, kuma Ya dawo da mu cikin aminci zuwa ƙasarmu Nigeria.