Kannywood

Bayan Auren Rahama Sadau da Adam A. Zango – Sabon Aure Zai Girgiza Kannywood

Bayan auren fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau, wanda ya daurewa mutane kai matuka domin ba a yi wani dogon lokaci da jita-jitar cewa ba a kawo mata aure kusa ba – sai aka wayi gari ana taya ta murna.

Haka zalika, jarumin Kannywood Adam A. Zango, shi ma ya kara aure a karo na uku, kuma abin ya faru ne a daidai lokacin da yake fama da rashin lafiya. Wannan ma ya haifar da cece-kuce da tattaunawa a tsakanin masoya da mabiyan fina-finan Hausa.

A halin yanzu kuma, ana ta jita-jita cewa za a yi wani aure a Kannywood wanda zai girgiza masana’antar baki ɗaya. Masu tsegumi suna cewa wannan auren ne wanda zai tashi kan kowa, ya fi kowanne aure jan hankalin al’umma.

To a ganin ku, wacece ko wanene zai yi wannan aure da ake ta yayatawa a kafafen sada zumunta?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button