Na fara sha’awar sana’ar film ne tun ina karama – Kilishi Ta Labarina

Tun ina ƙarama nake jin sha’awar harkar fim a zuciyata. Ban yi dogon karatu ba—iya sakandare na kammala—amma Alhamdulillah, rayuwa ta koya min darussa masu yawa, musamman yadda ake mu’amala da mutane.Na yi aure, daga baya na fuskanci jarabawa har ta kai ga rabuwa da mijina.
A wannan lokacin ne na haɗu da wata mace mai suna Hajara, wacce yanzu haka kwamishiniya ce a jihar Bauchi. Ita ce ta kai ni wajen Hayas Film Production, daga nan kuma aka tura ni zuwa Lenzcup. Daga bisani yayana ya samo min aikin rediyo, duk kuwa da cewa ban sanar da iyali ba.Na fara fitowa a fim din Hausa ta cikin shirin Babban Kasa.
Wannan ne karon farko da na taɓa ganin jaruma Daso a zahiri—na yi murna har na buga kaina da murfin motar saboda kallonta!Sai dai kalubale na farko ya zo lokacin da nake Kano—inda na faɗa wa wata lalata cewa ina son yin fim, ita kuma ta je ta sanar da iyayena. Amma abin da ya fi burge ni shi ne, mahaifina ya ji an yi hira da ni, bai yi fushi ba, saboda ban boye yaren da nake yi da asalin inda na fito ba.
Ya ce na ci gaba da fim dina, Allah Ya sa in samu albarka.A fina-finan Indiya, har yanzu mutum mai mugunta shi yakan fi birge ni saboda yadda ake nuna salon sa a fim. A harkar fim, abin da yafi bani wahala shi ne yawan zuwa chanja kaya saboda ɗaukar wurare daban-daban.Abin da ya fi faranta min rai shi ne, duk da cewa na rasa mahaifi da mahaifiya, idan na yi wani abu mai kyau, ina jin kamar na yi musu. Wannan na bani kwarin gwiwar ci gaba.Ina da burin zama kamar matar wani ɗan majalisa daga nan Jos, Laylah Ali Othman—wacce ta shahara wajen kyautatawa da taimakon mutane. Ina fatan in zama mai taimako da alheri ga al’umma.Shawarata ga dukkan ‘yan fim ita ce: “Mu ji tsoron Allah a duk inda muke da duk abin da muke yi.”
Allah Ya yi mana albarka a sana’armu, Ya kuma tabbatar mana da mutunci a idon jama’a