Kannywood
Hotunan Jarumar Kannywood Hadiza Gabon Sun Dauki Hankula

Fitacciyar jaruma a masana’antar Kannywood, Hadiza Ali Gabon, wadda aka fi sani da Hadiza Gabon, ta saki wasu sabbin hotuna a shafinta na Instagram waɗanda suka dauki hankalin masoyanta da mabiyanta.

A kwanakin nan, Hadiza Gabon ta rika janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta, musamman bayan da aka lura ta rage kiba sosai. Wannan sauyi ya sa mutane da dama ke bayyana mamaki da kuma tofa albarkacin bakinsu game da sabon yanayinta.

Wasu daga cikin magoya bayanta sun yaba da sabon kamanninta, suna cewa ta kara kyau da kyan gani, yayin da wasu kuma ke nuna sha’awa su san dalilin sauyin.