Kannywood
Fitaccen Mai Sarrafa Haske a Fina-Finai, Ahmad Kafi Giwa, Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Ahmad Kafi Giwa, wanda aka fi sani da “Ka fi Giwa Nama”, ya rasu yau sakamakon haɗarin mota da suka yi a kan hanyarsu ta dawowa daga Suleja. Allah ya ji ƙan sa.
Ahmad mutum ne mai matuƙar kirki, mai fara’a da murmushi a ko da yaushe. Babu wanda ya taɓa samun matsala da shi, domin ba shi da husuma, kuma zuciyarsa a buɗe take ga kowa.
Duk da tsokanar da ake masa tun yana ƙarami, bai taɓa nuna fushi ko ɓacin rai ba – hakan ya sa sunan ya zama ɓangare na rayuwarsa.Allah ya jikan sa da rahama, ya haskaka kabarinsa, ya yafe masa dukkan kura-kuransa, ya kuma saka masa da Aljanna Firdausi.
Allah Ya ba iyalansa da abokansa haƙurin jure wannan babban rashi.









